Malcolm Clarke, wani shahararren darektan fim dan kasar Birtaniya
2021-12-10 16:35:45 CMG
Ni ne mai jagorantar shirin Bello Wang, ina farin cikin kasancewa tare da ku. A kwanan baya na tafi birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin, don watsa labarai game da wani taron da ya gudana a can mai taken “Fahimtar kasar Sin”, inda na yi hira da wasu manyan kusoshi na kasashe daban daban, wadanda suka fahimci yanayin da kasar Sin ke ciki sosai. A cikin shirinmu na yau, bari ku saurari hirar da na yi da daya daga cikin wadannan mutane, mai suna Malcolm Clarke, wani shahararren darektan fim dan kasar Birtaniya.