logo

HAUSA

Sojojin Najeriya sun ceto 'yan sanda 20 da wasu 'yan bindiga suka sace

2021-12-10 10:35:29 CRI

Sojojin Najeriya sun ceto 'yan sanda 20 da wasu 'yan bindiga suka sace_fororder_211210-yaya 2-Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kubutar da 'yan sanda 20 da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da su, a wani hari na baya-bayan nan da suka kai kan wani ofishin 'yan sanda a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin kasar.

Bernard Onyeuko, ya shaidawa taron manema labarai a Abuja cewa, an yi garkuwa da ’yan sanda ne, lokacin da wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne, suka kai hari a kwanan baya a ofishin ’yan sanda a garin Buni Yadi na jihar Yobe.

Ya ce, an yi nasarar kubutar da ’yan sandan ne, a wani samame da sojojin suka kaddamar a yankin arewa maso gabas cikin makonni biyu da suka gabata. Sai dai bai yi wani karin bayani game da takamammen ranar da aka ceto su ba.

Jami’in ya ce, dabarun da sojojin suka yi amfani da su, sun taimaka wajen korar ’yan ta’addan daga sansanonin su, har ma suka mika wuya.  (Ibrahim Yaya)