logo

HAUSA

An gudanar da taron raya tattalin arzikin kasar Sin na shekarar badi

2021-12-10 19:44:05 CRI

An gudanar da taro game da ayyukan raya tattalin arzikin kasar Sin na shekara shekara a birnin Beijing. fadar mulkin kasar.

Taron wanda ya gudana daga ranar Laraba zuwa Juma’ar nan, ya hallara jagororin kasar, dake fatan tsara muhimman matakan bunkasa ayyukan raya tattalin arzikin kasar a shekarar 2022 dake tafe.

Cikin jawabin sa yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi bitar ayyukan raya tattalin arziki da kasar ta aiwatar a bana, tare da fayyace halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a yanzu, da kuma shirin da ake yi na tunkarar ayyukan raya tattalin arzikin kasar a shekara mai zuwa.(Saminu)