Amurka na wasa da wuta a aniyarta ta haifar da tashin hankali a zirin Taiwan
2021-12-09 19:26:48 CRI
Ko shakka babu a yau Amurka ta riga ta tsara taron da ta yiwa lakabi da "Taron dimokaradiyya". Burin ta shi ne, tallafawa masu yayata manufar "’yantar da yankin Taiwan". Sau da yawa ‘yan siyasar Amurka sun rika maimaita wannan manufa. Alal misali, mashawarcin fadar gwamnatin Amurka game da harkokin tsaro Jake Sullivan, ya furta wata barazana, cewa Amurka za ta yi duk mai yiwuwa don ganin har abada, ta hana babban yankin Sin ikon mulkar yankin Taiwan.
Wannan kuma na zuwa ne, bayan da kasar ta furta batun mamayar yankin Taiwan a kwanakin baya, inda Amurka ta yi yunkurin karkatar da tunanin al’umma, da nufin shafawa kasar Sin kashin kaji, da kawo tarnaki ga zaman lafiya da daidaito a zirin Taiwan, tare da yiwa manufar Sin ta dinkewa wuri guda karan tsaye.
Mr. Sullivan ya yi zargin cewa, matakan da Amurka ta aiwatar a yankunan tekun Indonesia da Pacific, cikin watanni 8 da suka gabata, na da nufin dakile matakin kasar Sin ne na yin mamaya. Ko shakka babu wadannan kalamai ne marasa tushe. Domin kuwa shaidu da dama sun tabbatar da cewa, matakan da Amurka da Taiwan ke dauka, tamkar wasa ne da wuta, kuma hakan ya zamo tushen haifar da yanayin zaman dar dar a zirin Taiwan. (Saminu)