logo

HAUSA

Jami’in MDD ya yi Allah wadai da hari kan dakarun wanzar da zaman lafiya a tsakiyar Mali

2021-12-09 11:13:59 CRI

Jami’in MDD ya yi Allah wadai da hari kan dakarun wanzar da zaman lafiya a tsakiyar Mali_fororder_211209-Mali

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da harin boma bomai na ranar Laraba wanda aka kaiwa ayarin motocin dakarun shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Mali, inda ya yi sanadiyyar kashe dakarun wanzar da zaman lafiyar bakwai ’yan kasar Togo sannan wasu uku kuma sun samu munanan raunuka, a cewar kakanin MDD.

Sakatare janar din ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan mutanen da harin ya yi sanadiyyar rayukansu, da gwamnati da kuma al’ummar kasar Togo. A sanarwar da ya fitar, kakakin MDDr Stephane Dujarric, ya yi fatan samun warka cikin hanzari ga wadanda suka samu raunuka.

Guterres, ya jaddada aniyar MDD na cigaba da nuna goyon baya ga kasar da kuma al’ummar Mali, wanda ya hada da karfafa yawan dakarun aikin wanzar da zaman lafiyar don kiyaye rayukan fararen hulda a tsakiyar Mali da kuma taimakawa dabarun da gwamnatin ke tsarawa don tabbatar da zaman lafiyar shiyyar. (Ahmad)