logo

HAUSA

Jami'in Afirka ta kudu: Kauracewa gasar Olympics ta lokacin sanyi, siyasa ce kawai

2021-12-09 10:38:54 CRI

Jami'in Afirka ta kudu: Kauracewa gasar Olympics ta lokacin sanyi, siyasa ce kawai_fororder_211209-SA

Mataimakin babban darektan sashen kula da harkokin Asiya da Gabas ta Tsakiya a hukumar kula da hadin gwiwa da huldar kasashen duniya ta kasar Afirka ta Kudu Anil Sooklal ya bayyana cewa, kauracewa halartar gasar Olympics ta Beijing ta shekarar 2022 da jami’an wasu kasashe za su yi, siyasa ce kawai.

Sooklal ya bayyana rashin jin dadinsa kan matakin da wasu kasashe suka dauka, na sanya siyasa a harkokin wasanni na kasa da kasa.

Duk da haka, Sooklal ya ce, yana da kwarin gwiwa cewa, sama da 'yan wasa 15,000 sun nuna aniyarsu ta shiga gasar a shekara mai zuwa. Ya kara da cewa, yana da kwarin gwiwar cewa, kasar Sin, za ta gabatar da wani gagarumin biki a shekara mai zuwa. (Ibrahim Yaya)