logo

HAUSA

Xi ya aikawa takwararsa ta Tanzaniya sakon taya murnar cika shekaru 60 da samun 'yancin kan Tanganyika

2021-12-09 11:48:35 CRI

Xi ya aikawa takwararsa ta Tanzaniya sakon taya murnar cika shekaru 60 da samun 'yancin kan Tanganyika_fororder_211209-Xi

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikawa takwararsa ta kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan sakon taya murna, dangane da cika shekaru 60 da samun 'yancin kan Tanganyika.

A cikin sakon nasa, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, bisa kokarin gwamnatocin Tanzaniya da suka shude da daukacin al'ummarta, kasar Tanzaniya ta samu ci gaba sosai, kuma nasarorin da aka samu, sun kasance masu ban mamaki. Ya ce, kasashen Sin da Tanzaniya sun kulla zumunci da alaka mai zurfi, a cikin 'yan shekarun nan. Haka kuma, kasashen biyu sun karfafa amincewa da juna a fannin siyasa, da zurfafa hadin gwiwar moriyar juna a fannoni daban daban. Shugaba Xi ya ce, ina mai da hankali sosai kan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Tanzaniya, kuma ina fatan yin aiki tare da shugaba Hassan, domin ciyar da hadin gwiwar Sin da Tanzaniya ta samun moriyar juna, da nasara tare a dukkan fannoni zuwa wani sabon matsayi. (Ibrahim)