logo

HAUSA

Bai Kamata A Mayar Da Gasar Olympics Wani Dandalin Siyasa Ba

2021-12-09 17:13:03 CRI

Bai Kamata A Mayar Da Gasar Olympics Wani Dandalin Siyasa Ba_fororder_hoto

Bisa taken gasar Olympics, wato "Sauri karfi da kasancewa tare", kowa na iya fahimtar ruhin wannan muhimmiyar gasa, wadda ke zama wani muhimmin dandalin gudanar da wasanni a mataki na kasa da kasa, mai kunshe da burin kasancewar sassan duniya baki daya “tsintsiya madaurin ki daya”.

To sai dai kuma, a wannan gaba da ya rage ‘yan makwanni a bude gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu da birnin Beijing zai karbi bakunci ta shekarar 2022, hankula na kara karkata ga yadda wasu kasashen yamma, ke ta hankoron keta manufar gasar na hade kan dukkanin sassa waje guda.

A baya bayan nan, an ga yadda Amurka da wasu kawayen ta suka bayyana aniyar su, ta hana jami’an su halartar gasar dake tafe, wanda hakan ke nufin wadannan kasashe na yammacin duniya, na fatan yin amfani da zuwan wannan muhimmiyar gasa, domin bude wani sabon babi na cacar baka, da yada karairayi, tare da yunkurin muzgunawa kasar Sin.

Ko shakka ba bu, mazarta da masu fashin baki, sun dukufa wajen wayar da kan al’ummun duniya game da manufar wadannan kasashe na yamma, wadanda tuni aniyar su ta fakewa da kare hakkin bil adama domin suka, da tsoka baki cikin harkokin gidan Sin ta jima da bayyana a fili.

A baya bayan nan, masu ruwa da tsaki a harkar wasanni, ciki har da kakakin kwamitin shirya gasar wasannin Olympics da birnin Beijing zai karbi bakunci a shekarar 2022, sun bayyana damuwa, da rashin amincewa da matakin Amurka da kawayen ta, suna masu bayyana matakin a matsayin kokarin rushe ruhin gasar ta Olympics, tare da siyasantar da harkar wasanni.

Abun lura a nan shi ne, yayin da wasu sassan duniya ke kokarin aiwatar da dukkanin manufofi da ka iya taimakawa wajen hade kan duniya, da wanzar da zaman lafiya da lumana, da cimma nasarar kafa kyakkyawan yanayin rayuwar bil adama mai makomar bai daya, wasu kasashen na daban kuwa, ba su da wani buri illa haifar da baraka, da kafa kawancen muzgunawa wasu kasashe, inda a zahiri muke ganin hakan a yanzu, karkashin wannan cacar baka da Amurka ta bullo da ita.

Ko shakka ba bu, wannan mataki na Amurka abun a yi tir da shi ne, kuma zai ci gaba da kasancewa shaida, dake nuna aniyar kasar da ‘yan kanzaginta na haifar da baraka ga duniya. (Saminu Hassan)