logo

HAUSA

Wang Yi ya gabatar da jawabi a taron dandalin dimokaradiyya na Bali

2021-12-09 19:33:43 CRI

A yau Alhamis ne babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, a dandalin dimokaradiyya da aka kira daga lardin Bali dake kasar Indonesia.

Cikin jawabin na sa, mai taken "Bunkasa ruhin hakikakin dimokaradiyya da samar da kyakkyawar makoma ga bil adama", Wang Yi ya ce dimokaradiyya mallakin daukacin bil adama ce. Kuma ba wata kasa dake da ikon mallakar ta, domin kuwa hakki ce ta daukacin al’ummun duniya. Ya ce ma’aunin gane ko wata kasa na gudanar da dimokaradiyya ko a’a, ya ta’allaka ne ga batun ko ‘yan kasar na jagorantar kan su ko a’a. (Saminu)