logo

HAUSA

Gayyatar gujajjen dan aware taron dimokaradiyya yiwa dimokaradiyya karsan tsaye ne

2021-12-08 20:08:45 CRI

Gayyatar gujajjen dan aware taron dimokaradiyya yiwa dimokaradiyya karsan tsaye ne_fororder_amurka

Wasu rahotannin baya bayan nan sun bayyana cewa, dan awaren nan na yankin Hong Kong Luo Guancong, wanda ya tsere daga yankin domin kaucewa fuskantar shari’a ya samu gayyyata daga Amurka, inda aka ce wai, zai gabatar da jawabi a taron da Amurkar ta kira da sunan kare dimokaradiyya.

Masharhanta da dama na mamakin yadda Amurka ta amince ta baiwa gujajjen dan aware damar zama bakon ta, wanda hakan ya kara fayyace mummunar manufar kasar, ta baiwa wadanda ake zargi da aikata laifi kariya, tare da kokarin tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin da sunan kare dimokaradiyya. Kaza lika hakan ya nuna irin baki biyu, da munafurcin dake tattare da salon dimokaradiyyar Amurka.

Shin wane ne ma Luo Guancong? Wannan mutum dai dan asalin yankin Hong Kong ne dake rajin ballewar yankin daga kasar Sin. Ya kuma sha furta kalamai na ingiza mutane, musamman matasa su aikata laifuka a Hong Kong. A ranar jajiberin fara aiwatar da dokar tsaron yankin Hong Kong ne kuma, Luo Guancong ya tsere zuwa ketare, ya kuma ci gaba da gudanar da ayyukan da ya saba na ingiza tashin hankali a Hong Kong.

A watan Yulin shekarar 2020, ‘yan sandan Hong Kong sun yi yunkurin cafke Luo Guancong tare da wasu masu haifar da tarzoma a Hong Kong, wadanda suka tsere zuwa ketare, suka ci gaba da hadin gwiwa da wasu ‘yan kasashen waje, wajen rura wutar tashin hankali a HK.  (Saminu)