logo

HAUSA

Demokiradiyar kasar Sin ya dace da yanayin kasa da al’ummarta

2021-12-08 09:31:13 cri

A karshen makon da ya gabata, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fidda takardar bayani mai taken “Dimokaradiyyar Kasar Sin.” Takardar ta yi nuni da cewa, dimokaradiyyar kasar Sin, dimokaradiyya ce ta al’umma, wato al’umma ne jigo da ginshikin harkokin kasar. Kana dimokradiyya hakki ne na al’ummomin kasa baki daya, ba hakki ne na wasu kasashe na musamman ba. A don haka, al’ummun kasa ne ya dace su tantance yadda ake bin tafarkin dimokaradiyya a kasar. Haka kuma, bai kamata wasu kasashe su rika yin korafi ba, kan ko kasa tana bin tafarkin dimokaradiyya, ko a’a, kasashen duniya ne ya dace su tantance, ba wai wasu ’yan tsirarun kasashe su rika yin shisshigi ba. 

Demokiradiyar kasar Sin ya dace da yanayin kasa da al’ummarta_fororder_211208世界21046-hoto1

Akwai mabambantan hanyoyi da ake bi domin tafiyar da harkokin dimokaradiyya. Don haka, bai kamata a yi amfani da mizani daya don tantance mabambantan tsare-tsaren siyasa da al’adun siyasa iri-iri na duniya ba, domin yin hakan, ba shi ne ainihin dimokaradiyya ba. Ma’anar dimokaradiyya ga kasar Sin da al’ummar Sinawa, ta yi hannun riga da yadda wasu kasashen yammacin duniya ke ikirarin su ne jagororin kafa tsarin dimokaradiyyar duniya.

Demokiradiyar kasar Sin ya dace da yanayin kasa da al’ummarta_fororder_211208世界21046

Demokaradiyya wani tsari ne na shugabancin al’umma da tafiyar da harkokin kasa, ko da yake ma’ana da manufar demokaradiyya ya dogara ne da yadda mahukunta kowace kasa ke gudanar da kasar ta yadda zai dace da yanayin tarihi, al’adu, tattalin arziki, da yanayin zaman rayuwar al’umma, kuma bisa dacewa da yanayin da kasar ke ciki. Wannan yana daga cikin manyan dalilan da kasar Sin ke kara jaddada matsayinta game da hakikanin manufar demokaradiyya a mahangar kasar. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)