logo

HAUSA

Yawan kunshin kayayyakin da aka aika a kasar Sin ya zarce biliyan 100

2021-12-08 14:18:17 CRI

Yawan kunshin kayayyakin da aka aika a kasar Sin ya zarce biliyan 100_fororder_918682234676707360 (1)

Alkaluman da hukumar gidan waya ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a shekarar 2021 da muke ciki, a karo na farko, yawan kunshin kayayyakin da aka aika a kasar ya zarce biliyan 100, abin da ya sa kasar ta kasance ta farko a wannan fanni a duniya cikin shekaru 8 a jere.

Mataimakin shugaban hukumar gidan waya ta kasar Chen Kai ya ce, a sakamakon bunkasuwar sashen aika kunshin kayayyaki, an kuma samu ci gaba na gani, ta fannonin sayar da kayayyaki ta yanar gizo, da amfanin gona, da kere-kere, da sayar da kayayyaki ta yanar gizo zuwa ketare.

Ba da jimawa ba, za a kammala gina tsarin aikin tura kunshin kayayyaki wanda zai game fadin kasar da ma sassan duniya. Yanzu haka kuwa, kusan tsarin ya game dukkanin garuruwan kasar, wanda ke samar da hidimomi ga al’umma kusan miliyan 700 a kowace rana, tare da samar da karin guraben aikin yi sama da dubu 200 a kowace shekara.

A wannan shekara, an fi aikewa da amfanin gona daga karkara zuwa birane, da kuma kayayyakin masana’antu daga birane zuwa karkara, kuma yanzu haka kusan ana aikawa da sakwannin kayayyakin miliyan 100 a kowace rana zuwa yankunan karkara, tare da aikawa da amfanin gona zuwa birane, don haka, hidimar aikawa da kunshin kayayyaki yana taka muhimmiyar rawa, wajen kiyaye nasarorin da aka samu a fannin saukaka fatara, da ma farfado da yankunan karkara. (Lubabatu)