logo

HAUSA

Najeriya ta tabbatar da karin mutum 3 da suka kamu da COVID-19 nau’in Omicron

2021-12-08 13:58:11 CRI

Najeriya ta tabbatar da karin mutum 3 da suka kamu da COVID-19 nau’in Omicron_fororder_i01-Nigeria confirms 3 more Omicron cases of COVID

Hukumomin Najeriya a ranar Talata, sun tabbatar da karin wasu mutane uku da suka kamu da nau’in Omicron na COVID-19, wanda ya kawo adadin wadanda suka kamu da nau’in cutar zuwa shida a kasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka.

Shugaban hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) Ifedayo Adetifa, ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, kawo yanzu dukkan wadanda suka kamu da nau’in cutar a kasar, mutane ne da ke da tarihin yin balaguro zuwa Afirka ta Kudu a watan Nuwamba.

Adetifa ya ce cibiyar kula da lafiyar jama'a ta kasa, za ta ci gaba da daidaita ayyukan sa ido kan kwayoyin halitta a duk fadin kasar, don nazartar dukkan samfuran cutar ta COVID-19 da aka dauka daga matafiya, da suke shigowa cikin kasar daga sassa daban-daban na duniya.

Ya ce duk da haka, nau’in Delta na cutar, shi ne mafi girman bambance bambancen ya zuwa yanzu, saboda ba mu ga wani sabon nau’in cutar da ya dara nau’in Omicron, kamar yadda aka gani a wani wuri ba. (Ibrahim)