logo

HAUSA

An kammala dukkan gwaje-gwaje a yankin da za a gudanar da gasar wasannin Beijing 2022 Olympic

2021-12-08 11:25:44 CRI

An kammala dukkan gwaje-gwaje a yankin da za a gudanar da gasar wasannin Beijing 2022 Olympic_fororder_src=http___ww4.sinaimg.cn_mw690_002uLDeXly1gvttw5u7d5j60eg099q4m02&refer=http___www.sina

A karshen wanan mako an kammala dukkan gwaje gwajen da suka kamata a yankin da za a shirya gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Beijing 2022 Olympic da ta nakasassu, inda gwaje gwaje ya shafi wajen da aka tanadawa mahalarta 2,415, wanda ya kunshi gidajen kwana, da kantunan dafa abinci, da cibiyoyin gwajin annobar COVID-19 (PCR).

 

A bangaren kudu na cibiyar wasannin Olympic ta kasa, yankin na kunshe da gine gine 20, wanda zai karbi bakuncin mahalarta gasar Olympics kimanin 2,338, da kuma mahalartar gasar nakasassu kimanin 1,040.

 

Ju Qiang, mataimakin darakta mai kula da sashen gidajen kwana na yankin, ya bayyana cewa, ’yan wasa za su iya daidaita girman gadajensu wajen kara tsawonsu har zuwa mita 2.4 domin su ji dadin barci da samun kyakkyawan hutu.

 

A cewar Ji Ye, mataimakin daraktan sashen kula da abinci na yankin gudanar da wasanin, yankin zai dinga samar da isasshen abinci ga ’yan wasan a lokacin gudanar da gasar, kuma akwai jadawalin nau’ikan abinci har guda 678 da za a samar ga ’yan wasan da suka fito daga bangarorin al’adu daban daban na duniya, domin biyan muradunsu da kuma yanayin nau’ikan abincin da jikinsu ke bukata, sannan kuma an bayar da kulawa ga tsarin abinci na mabiya addinai daban daban.

 

Sin: Siyasantar da wasannin motsa jiki ya saba wa ruhin Olympics

 

A cewar wasu rahotanni, shugaban kasar Amurka Biden ya tabbatar da cewa, yana tunanin "kauracewa gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing a diflomasiyance. Dangane da wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a gun taron manema labaru na yau da kullum Jumma’ar nan cewa, siyasantar da wasannin motsa jiki ya sabawa tsarin wasannin Olympics, kuma yana cutar da muradun 'yan wasa daga dukkan kasashen duniya. Batun Xinjiang harkokin cikin gidan kasar Sin ne, kuma ba za a lamunci makiyan kasar Sin daga waje su tsoma baki ta kowace fuska ko hanya ba.

 

 

Manchester United Ta Sallami Solksjaer

 

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sallami mai horas da ‘yan wasa Ole Gunnar Solskjaer bayan kungiyar ta sha kashi a hannun Watford da ci 4-1 a jiya Asabar.

 

Hakan ya sa Manchester United ta dawo ta bakwai a gasar firimiya da maki 12 bayan wasanni 12 da kungiyar ta buga. Sau daya Manchester United ta ci wasa a league bakwai da ta buga, ciki har da kashin da Liverpool ta ba ta da ci 5-0 da kuma yadda da Manchester City ta lallasa ta da 2-0.

Solskjaer mai shekara 48 ya maye gurbin Mourinho a matsayin kocin wucin gadi a Disambar 2018. Sai dai daga baya an ba kocin ɗan asalin kasar Norway cikakken kwantiragi a Maris din 2019 na tsawon shekara uku, inda a watan Yuli ya saka hannu a sabuwar yarjejeniya da kulob ɗin zuwa 2024. A yanzu Michael Carrick ne kulob din ya zaba a matsayin sabon koci na wucin gadi wanda zai ci gaba da jagorantar kulob din.

 

 

 

 

Wadanda Za Su Taimakawa Xavi A Barcelona

 

Ranar Talata Xavi Hernandez ya fara jan ragamar atisayen Barcelon a matakin sabon kocinta kuma Xavi tsohon dan wasan Barcelona ya amince da kunshin yarjejeniyar kammala kakar bana da kara guda biyu bayan nan. Ga jerin wadanda zai gabatar da aikin tare da su a Barcelona.

 

Babban koci: Xavi Hernandez. Mataimaki na daya: Òscar Hernández. Mataimaki na biyu: Sergio Alegre. Mai kula da kuzarin ‘yan wasa: Ibán Torres. Kocin masu tsaron raga: José Ramon De la Fuente.

 

Masu kula da nagarta da kwazo: Sergio Garcia da Toni Lobo da kuma Xavid Prats Xavi zai fara jan ragamar Baracelona wasan hamayya da za ta buga da Espanyol ranar 20 ga watan Nuwamba a gasar La Liga kuma Barcelona mai kwantan wasa tana ta tara a kan teburin gasar La Liga da maki 17, bayan kammala karawar mako na 13.

Barcelona ta gabatar da Xavi a gaban magoya bayanta da kuma ‘yan jarida a filin wasanta ranar Litinin, wanda ya maye gurbin Ronald Koeman da ta sallama, kuma tuni Xavi ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen kakar wasa ta 2024.

 

Dan kasar ta Sifaniya mai shekara 41 ya fara horar da Al Sadd tun daga shekara ta 2019, wanda ya amince ya karbi aikin jan ragamar Barcelona ranar Juma’a kuma a baya ya yi wa Barcelona wasanni 767 a kungiyar ya lashe kofi 25 a shekara 17 da ya yi sannan daga nan ya koma Al Sadd a matakin dan wasa a 2015, sannan ya zama kocinta