logo

HAUSA

Albarkacin Kaza….

2021-12-08 19:25:04 CRI

Albarkacin Kaza…._fororder_211208-sharhi-Ibrahim-hoto

A bana ne, kasar Sin ta cika shekaru 20 da zama mambar kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO. A cikin shekaru 10 da suka gabata, bayanai sun tabbatar da cewa, kasar Sin ta ba da gudummawar kashi 20 bisa 100 na karuwar tattalin arzikin kasashen Afirka.

Kasancewar mambar WTO, mai martaba dokoki da ka’idojin wannan kungiya, ya sa kasar Sin tsayawa tsayin daka wajen kare tsarin ciniki a tsakanin sassa daban daban, lamarin da ya zama abin koyi ga sauran kasashe maso tasowa. Haka kuma a matsayinta na mambar kungiyar WTO, kasashe da dama suna koyi da fasahohin kasar Sin, domin neman ci gaba ta hanyoyi masu dacewa da kuma bisa tsarin kungiyar WTO.

Alkaluma sun nuna cewa, daga shekarar 2000 zuwa wannan lokaci, darajar hajojin da kasar Sin ta shigo da su cikin kasarta daga kasashen Afirka, ya kai dalar Amurka triliyan 1.2, yayin da ta fitar da hajoji zuwa kasashen Afirka da darajarsu ta kai dalar Amurka triliyan 1.27. Cikin ’yan shekarun nan kuma, darajar cinikayya a ko wace shekara tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, ya kai dalar Amurka biliyan 200, kana adadin amfanin gona da kasar Sin ta shigo da su daga kasashen Afirka, yana karuwa cikin sauri, inda matsakaicin karuwar adadin cikin shekaru 5 da suka gabata, ya kai kashi 11.4 bisa dari.

Masu fashin baki na cewa, duk da adawa da ma kafar unguwa da wasu kasashen yamma ke yiwa tsakanin kasancewar bangarori daban-daban, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kare tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban, matakan da ya taimakawa kasashen Afirka wajen neman bunkasuwa da kansu. Albarkacin Kaza, kadangare kan sha ruwan kasko.

Hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka bisa tsarin ciniki tsakanin bangarori daban daban, zai taimakawa kasashen Afirka wajen yiwa tattalin arzikinsu gyaran fuska. Sai dai masu adawa da alakar Sin da kasashen Afirka, ba sa farin ciki da irin ci gaban da sassan biyu ke samu karkashin kungiyar WTO, da ma sauran fannonin da Sin da Afirka da kuma Sin da raguwar kasashe masu tasowa suke samu. (Ibrahim Yaya)