logo

HAUSA

Tuna da Liang Xiaoxia, ma’aikaciyar jinya ce ta kungiyar aikin jinya ta yaki da annobar COVID-19

2021-12-07 14:08:17 cru

Liang Xiaoxia, ma'aikaciyar jinya ce a wani asibitin dake birnin Nanning na lardin Guangxi dake kudancin kasar Sin, wadda ta taba ba da roko har sau biyu don tafiya lardin Hubei, wanda ya taba kasancewa wurin da ya fi fama da annobar COVID-19, don taimakawa yaki da annobar. A ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2020, Liang Xiaoxia ba zato ba tsammani ta suma yayin da take aiki a wani asibitin na Wuhan, bayan duk kokarin ceto ya ci tura, abin takaici ta mutu, a lokacin dai shekarunta na haihuwa sun kai 28 ne kawai.

A watan Yunin bana, aka kammala dakin tunawa da Liang Xiaoxia a asibitin da take aiki wato asibitin jama’a na 6na Nanning, kuma an soma bude shi ga jama'a, inda ake nuna lambobin yabo da Liang Xiaoxia ta samu, da abubuwan da ta taba amfani da su a lokacin rayuwarta...Kowane abu yana "bayyana" labarunta masu burgewa.

Mataimakin shugaban asibitin jama’a na 6, Deng Hongda ya ce, "Asibitinmu yana da ma'aikata sama da 400, amma Liang Xiaoxia ta burge ni musamman." Ya kara da cewa, Liang Xiaoxia ta yi aiki cikin himma da kwazo, kuma ta zama kashin baya a Sashen Kula da Cututtukan Numfashi jim kadan bayan ta fara aikin. Duk abokan aikinta da marasa lafiya sun yaba mata kwarai da gaske.

Tuna da Liang Xiaoxia, ma’aikaciyar jinya ce ta kungiyar aikin jinya ta yaki da annobar COVID-19_fororder_src=http___www.aitmy.com_static_pic_1_20_05_29_1590712204_57802&refer=http___www.aitmy

Bayan barkewar annobar COVID-19, asibitin jama’a na 6 na birnin Nanning, ya aika da rukunoni biyu masu kunshe da mutane 12 don su shiga cikin kungiyar Likitoci ta yaki da annobar ta lardin Guangxi don su tafi sahun gaba na tinkarar annobar a lardin Hubei.

Lokacin da aka dauki rukunin farko na masu aikin sa kai, jimillar kwararrun ma’aikatan lafiya 103 a asibitin sun gabatar da rokon shiga aikin nan. A karshe asibitin ya zabo mutane 10 daga cikinsu, Liang Xiaoxia na daya daga cikinsu saboda kwarewarta a fannin aiki.

Shugaban asibitin, Deng Hongda ya ce, a karshe, an sanar da cewa asibitin su na bukatar aika mutane 6 ne kawai, kuma sun tsaida kudurin aika ‘yan jam’iyyar kwaminis zuwa lardin Hubei. Da take sanin cewa, ba a zabe ta ba a takardar sunayen dake rukunin farko game da ba da tallafi ga lardin Hubei, Liang Xiaoxia ta garzaya don neman shugaba Deng Hongda, ta tambaye shi, me ya sa ba a zabe ta ba.

Domin kwantar da hankalinta, Deng Hongda da sauran shugabannin asibitin suka yi mata bayani na musamman. Bayan 'yan kwanaki, an samu sanarwar aikewa da rukuni na biyu na jami'an kiwon lafiya zuwa Hubei, kuma nan da nan Liang Xiaoxia ta sake neman yakin nan, a wannan karon kuma ta kawo takardar neman shiga jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.

A cikin takardar neman shiga jam’iyyar, Liang Xiaoxia ta rubuta kamar haka, “A lokacin da ake zabar ma’aikatan jinya cikin gaggawa zuwa Hubei domin aikin ba da agajin jinya, ‘yan jam’iyyar da ke asibitinmu sun ba da roko daya bayan daya, irin halayyarsu ta burge ni har ta zaburar da ni shiga jam’iyyar. A ko da yaushe zan nemi kaina bisa ka'idar ‘yan jam'iyyar Kwaminis, zan kuma yi aiki tukuru don jure wa gwaji a yakin da ake yi da annobar, tare da yin iyakacin kokari don samun nasarar rigakafin wannan annoba.”

A cikin aikinta na yau da kullum, Liang Xiaoxia tana ba da gudummawa sosai ga abokan aikinta tare da mai da hankali kan hadin kai. Daga shekarar 2016 zuwa ta 2019, Liang Xiaoxia ta kasance mutum daya tilo a asibitin da ba ta da hutun rashin lafiya da na biyan wata bukata a cikin shekarun hudu, kuma har yanzu ita ce wadda kwanakin aikin dare da ta yi suka fi yawa a asibitin.

Kusan dukkan abokan aikin ta a sashensu sun taba neman Liang Xiaoxia da ta cike gurbinsu wajen gudanar da aikin na wani dan lokaci. Liang Xiaoxia ta kan taimakawa abokan aikinta da ba su da lafiya ko kuma ke da matsala a gida. Yanzu, lokacin da aka ambaci Liang Xiaoxia, abokan aikinta da yawa hawaye ne ke barkewa daga idanunsu.

Tuna da Liang Xiaoxia, ma’aikaciyar jinya ce ta kungiyar aikin jinya ta yaki da annobar COVID-19_fororder_a72330f42b654b518b4d65b8973699d2

Mataimakiyar shugabar ma'aikatan jinya na sashensu Huang Liping, ta gayawa manema labarai cewa, sashensu ya kan samu majinyata da ke fama da matsalar motsi, a matsayinta na ginshikin ma'aikatan jinya na sashen, Liang Xiaoxia a ko da yaushe tana taimaka musu wajen debo tafasasshen ruwa da ba su abinci.

Huang Liping ta tuna cewa, wata rana, sun karbi wata maras lafiya cikin gaggawa, da ta shigo, sai ga tsohuwar nan ta suma, har ta kasa rike fitsari da kashi. Liang Xiaoxia ba ta ja da baya ba saboda kyama, kuma ta debo ruwa don taimakawa tsohuwar nan wajen tsaftace jikinta. Ta yi ta kulawa da tsohuwar ba tare da gajiyawa ba.”

An kafa wani sashen musamman ga yara masu fama da ciwon Karancin sinadarin Hb na cikin jini irin na Thalassemia a asibitin jama’a na 6 na birnin Nanning, yawan wadanda suke fama da ciwon da aka yiwa rajista a asibitin ya wuce 250. Liang Xiaoxia ta dauki yaran a nan a matsayin kannenta kuma tana kula da su sosai. Ta kan yi amfani da lokacin hutunta don ba da labari ga yaran, da koya musu wasanni masu ban sha'awa.

Mahaifiyar Liang Xiaoxia Qin Junxiao ta gaya wa manema labaru cewa, “Xiao Xia yarinya ce mai kirki. A lokacin da take karama, da ta ga irin wahalar da ‘yan uwanta da mazauna kauyen ke fama da su sakamakon rashin lafiya, sai ta yi fatan aiki a fannin likitanci da kiwon lafiya a nan gaba, da fatan za ta rage radadin masu fama da ciwo ta hanyar kokarin da take yi.” Bayan kammala jarrabawar shiga jami'a, Liang Xiaoxia ta zabi koyon fasahar jinya a jami’a, sannan ta tafi asibiti don yin aikin jinya bayan kammala karatu. Mahaifiyarta ta ce, “Gudunmawarta ta yi kyau, ina tunaninta sosai.”