logo

HAUSA

Najeriya na shirin cimma burin yiwa ’yan kasarta rigakafin COVID-19 nan da 2022

2021-12-07 14:00:06 CRI

Najeriya na shirin cimma burin yiwa ’yan kasarta rigakafin COVID-19 nan da 2022_fororder_211207-yaya 2-Nigeria

Sakataren gwamnatin tarayya Najeriya, Boss Mustapha ya bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kuduri aniyar yiwa kashi 70 cikin 100 na ’yan kasar allurar riga-kafin COVID-19 kafin karshen shekarar 2022.

Boss Mustapha ya bayyana haka ne, a taron koli na kasa kan cutar ta COVID-19 da aka gudanar a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Yana mai cewa, kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka, ta riga ta saka hannun jari a fannin alluran rigakafin da za su ishi sama da kashi 70 cikin 100 na al’ummarta kafin karshen shekara mai zuwa.

Boss Mustapha wanda shi ne shugaban kwamitin shugaban kasa kan yaki da annobar ta COVID-19, ya bayyana cewa, alluran rigakafin suna da kyau da kuma inganci, don haka yana da kyau jama’a su yi rigakafin cutar.

Taron mai taken "Kokarin kawo karshen kwayar cuta da sake farfadowa yadda ya kamata," ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a fannonin kiwon lafiya, da tattalin arziki, da tsaro, da tsara manufofi na kasar.

A cewar hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa, ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, sama da mutane miliyan 7.1 ne aka yi kashi na farko na rigakafin COVID-19, wanda ke wakiltar kashi 6.4 na adadin wadanda suka cancanta a Najeriya, yayin da kimanin mutane miliyan 3.8 suka karbi cikakkaciyar allurar rigakafi, wanda ke wakiltar kashi 3.4 na jimillar mutanen da suka cancanci karbar riga kafi a kasar. (Ibrahim Yaya)