logo

HAUSA

Sin: Kauracewa wasannin Olympics da jami’an diflomasiyyar Amurka za su yi ra'ayin siyasa na son kai

2021-12-07 15:57:06 CRI

Sin: Kauracewa wasannin Olympics da jami’an diflomasiyyar Amurka za su yi ra'ayin siyasa na son kai_fororder_olympics-2022

Mai magana da yawun tawagar kasar Sin dake MDD ya bayyana cewa, kauracewa gasar Olympics ta lokacin huturu da birnin Beijing zai karbi bakuncinta na shekarar 2022 da jami’in diplomasiyyar Amurka za su yi, wani shiri ne na siyasar son kai.

Kakakin wanda ba a bayyana sunansa ba, ya fada a cikin wata sanarwa cewa, wasannin Olympics na lokacin hunturu da ajin nakasassu na Beijing, taro ne na dukkan 'yan wasan motsa jiki da masu sha'awar wasannin hunturu a duniya. Kuma su ne ya kamata duniya ta san irin wainar da suke toyawa. Don haka, nasarar wasannin ba ta dogara kan halartar wasu tsirarun jami'an gwamnatocin kasashen duniya ba.(Ibrahim)