logo

HAUSA

Kasashen Sin da Saliyo sun yi alkawarin inganta hadin gwiwa a tsakaninsu

2021-12-07 14:01:07 CRI

Kasashen Sin da Saliyo sun yi alkawarin inganta hadin gwiwa a tsakaninsu_fororder_211207-yaya 3-Yang Jiechi

Shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio, jiya Litinin ya gana da babban jami'in diflomasiyyar kasar Sin Yang Jiechi, inda bangarorin biyu suka yi alkawarin inganta hadin gwiwarsu a fannoni daban daban.

A yayin taron ministoci karo na takwas na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC) da aka kammala a Dakar na kasar Senegal, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimman shawarwari kan gina al'ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a sabon zamani, da wasu manyan matakai, wadanda Yang ya ce, sun bayyana kudirin kasar Sin na son kara karfafa hadin kai da hadin gwiwa da kasashen Afirka.

A jawabinsa Yang Jiechi, mamban ofishin siyasa na kwamitin koli na JKS, kana daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS, ya ce kasar Sin na son hada kai da Saliyo, wajen aiwatar da shirin na FOCAC, da daidaita yarjejeniyoyin taron tare da bukatar ci gaban kasar Saliyo, da kuma kara inganta hadin gwiwa a fannonin da suka hada da yaki da annobar COVID-19, da aikin gona, da kiwon kifi, da ilimi, da ababen more rayuwa, da taimakawa kasar Saliyo wajen yaki da annobar COVID-19, da kuma farfado da tattalin arzikinta.  

A nasa bangaren, shugaba Maada Bio ya ce, kasar Sin ta ba da gudummawa sosai ga zaman lafiya da ci gaban duniya, kana ta zama abin koyi ga kasashe masu tasowa. Yana mai cewa, kasarsa tana tsayawa tsayin daka wajen martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma tana goyon bayan wasannin Olympics na lokacin sanyi na shekarar 2022 da birnin Beijing zai karbi bakunci.  

Shugaba Bio ya bayyana cewa, kasar Saliyo na maraba da sabbin tsare-tsare kan hadin gwiwar Sin da Afirka da shugaba Xi ya bayyana, a yayin bikin bude taron ministoci na FOCAC karo na takwas. Haka kuma, Saliyo na son inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa tsarin FOCAC, da bunkasa hadin gwiwa kan harkokin kasa da kasa, da kare halastattun hakkoki da moriyar Sin da Afirka, da na kasashe masu tasowa. (Ibrahim Yaya)