logo

HAUSA

Hadarin gamuwa da harbin bindiga na tarnaki ga dimokaradiyyar Amurka

2021-12-07 20:30:08 CRI

Hadarin gamuwa da harbin bindiga na tarnaki ga dimokaradiyyar Amurka_fororder_amurka

A ‘yan kwanakin baya ne wani matashi dan shekaru 15 da haihuwa, dake karatu a wata makarantar sakandare ta jihar Michigan a kasar Amurka, ya harbe ‘yan uwansa dalibai 4 har lahira. An ce iyayen matashin ne suka saya masa bindigar da ya yi harbin da ita, a matsayin kyautar bikin kirsimeti.

Alkaluman kididdiga na nuna cewa, Amurka ce a kan gaba, a jerin kasashe mafiya raunin dokokin amfani da bindiga, kuma al’ummar ta ne kan gaba a yawan masu mallakar bindiga a duniya, yayin da yiwuwa Amurkawa su hadu da hadarin harbin bindiga, ya ninka na sauran kasashe masu wadata da kusan ninki 25.

Amurka dai na daukar batun kare hakkokin jama’ar ta, a matsayin daya daga ginshikan yayata ingancin dimokaradiyyar ta, to sai dai kuma alal hakika, kare rayukan Amurkawa na kasancewa wani abu maras tabbas a kasar.  (Saminu)