logo

HAUSA

Sharhi: Demokuradiyyar Amurka da ke bautawa kudi ba demokuradiyya ta gaske ba ce.

2021-12-07 13:50:13 CRI

Sharhi: Demokuradiyyar Amurka da ke bautawa kudi ba demokuradiyya ta gaske ba ce._fororder_微信图片_20211207134841

“Kasar Amurka kasa ce da ke bin tsarin jari hujja, ba kasar da ke bin demokuradiyya ba ce.” Kishore Mahbubani, wani masani na dan kasar Singapore, shi ne ya fadi haka yayin da yake zantawa da manema labarai a kwanan baya. Ya ce, a Amurka, demokuradiyya na hidimtawa attajirai ne kawai, ma’ana tsari ne da ta fi karkata ga kudi da kuma neman iko. Wannan ba boyayyen abu ba ne,kowa ya san da haka.

Shaidu sun nuna cewa, kudi shi ne jigon siyasar Amurka, wanda ya shafi dukkan matakai na ayyukan zabe, da kafa doka, da ma gudanar da harkokin kasar. Kaso 91 bisa dari na ’yan majalissun kasar an zabe su saboda kudinsu. Wannan na nuna cewa, demokuradiyyar Amurka takara ne tsakanin attajirai.

Yau kusan shekaru 100 da suka gabata, babban alkalin kotun koli ta Amurka Brandeis Louis ya taba bayyana cewa, “A wannan kasa, akwai hanyoyi biyu, ko dai ta samu demokuradiyya, ko dukiya a hannun mutane kalilan, a don haka, zabi ya rage mata.” Yanzu siyasar kudi a Amurka, ta zama wata babbar matsala ga zamantakewar al’ummar kasar, wadda dake wahalar warwarewa. Don haka, batun wai gwamnatin Amurka za ta kira taron koli na demokuradiyya, yaudara ne. (Kande Gao)