logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta zargi Birtaniya da hana zirga-zirga a kan Omicron

2021-12-07 13:58:49 CRI

Gwamnatin Najeriya ta zargi Birtaniya da hana zirga-zirga a kan Omicron_fororder_211207-yaya 1-Nigeria Omicron

Gwamnatin Najeriya ta caccaki matakin da hukumomin Birtaniyya suka dauka, na hana matafiya daga Najeriya shiga kasarta, saboda gano bullar nau’in cutar COVID-19 na Omicron a kasar mafi yawan jama’a a nahiyar Afirka.

Ministan yada labarai da al'adu Lai Mohammed ya shaidawa taron manema labarai a Abuja, babban birnin Najeriya cewa, matakin da gwamnatin Birtaniya ta dauka na sanya Najeriya cikin jerin kasashe da ta haramtawa ’yan kasarta shiga cikin kasar, ba shi da madogara na kimiya, kuma dole ne a gaggauta soke shi, musamman ganin cewa, nau’in cutar bai samo asali daga kasar da ke yammacin Afirka ba.

Jami’in na Najeriyar ya lura cewa, ’yan kasar Burtaniya da mazauna kasar na da damar shigowa kasar daga Najeriya, yayin da aka haramta wa wadanda ba mazauna kasar ba. Yana mai aza ayar tambaya kan dalilan da suka sa aka sanya nau’ikan mutane biyu da suka fito daga kasa daya cikin yanayi daban-daban.  

Ministan ya ce, haramcin tafiye-tafiye, irin wanda aka dauka kan wasu kasashen Afirka, "wannan tamkar kamshin mutuwa ne" wanda kawai zai iya yin illa ga yunkurin da ake na shawo kan cutar ta COVID-19. Don haka, ya yi kira ga shugabannin duniya da su dauki na tsanaki kan batun samar da alluran rigakafi, a maimakon martanin da zai haifar da tsoro, maimakon mataki na kimiyya. (Ibrahim Yaya)