logo

HAUSA

Jami'an sojan Somaliya da na AU sun kara kaimi kan tattara bayanan sirri

2021-12-06 10:57:33 CRI

Jami'an sojan Somaliya da na AU sun kara kaimi kan tattara bayanan sirri_fororder_211206-AU-Ibrahim

Sojoji 20 na rundunar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar Tarayyar Afirka (AMISOM) da sojojin kasar Somaliya (SNA) jiya Lahadi suka kammala wani shirin atisaye na kwanaki hudu, da nufin kara kaimi kan fasahar tattara bayanan sirri dake da matukar muhimmanci wajen rage kaifin kungiyar ’yan ta'addar Al-Shabab a kasar.

Tawagar ta AU ta ce, manufar horon game da dabarun tattarawa da musayar bayanai, ita ce zurfafa hadin gwiwa wajen gudanar da ayyukan soji na hadin gwiwa kan 'yan ta'adda a Somaliya.

Kwamandan rundunar ta AMISOM Diomede Ndegeya ya jaddada muhimmancin kwas din ga ayyukan soji, yana mai cewa leken asiri ko bayanai na da matukar muhimmanci wajen gudanar da ayyukan soji, da AMISOM da kuma rundunar sojojin Somaliya (SNA).

Kwas din wanda gidauniyar J2 ta shirya, ya samu halartar jami’an rundunar sojojin Somaliya guda bakwai da kuma jami’an soji na AMISOM 13, wadanda aka zabo daga dukkan bangarorin.

Ndegeya ya ce, bayanan sirri na iya inganta tsare-tsare da yanke shawara, yana mai cewa halin da ake ciki a Somaliya, yana da sarkakiya kuma yana kara samun ci gaba, lamarin dake bukatar wayar da kan jama'a yadda ya kamata. (Ibrahim)