logo

HAUSA

Sin: Amurka ba ta da ikon fakewa da maganar dimokuradiyya tana ta da rikici a duniya

2021-12-06 20:12:16 CRI

Mai magana da yawon ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, mista Zhao Lijian, ya bayyana a yau Litinin cewa, tsarin dimokuradiyya na kasar Amurka, wani sakamako ne da kasar ta samu bisa gwajin da ta yi ita kadai a cikin gida, don haka ba dole ne ya zama mai dacewa da sauran kasashe ba. Saboda haka, kasar Amurka ba ta da ikon yin babakere game da mizanin dimokuradiyya, da fakewa da maganar dimokuradiyya wajen neman kulla kawance tare da wasu kasashe, da ta da rikici a duniya.

Ban da wannan kuma, dangane da wani rahoton da ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta gabatar, game da yanayin harkar dimokuradiyya a kasar Amurka, Zhao ya ce, dimokuradiyya ta daukacin bil Adama ce, kuma ba ta karkashin mallakar wata kasa ita kadai.

Kaza lika Zhao ya ce akwai dimbin hanyoyi daban daban, da za a iya bi wajen tabbatar da tsarin dimokuradiyya. Kuma idan aka nemi auna tsare-tsaren siyasa daban daban da mizani guda, hakan ba zai zama dimokuradiyya ba.    (Bello Wang)