logo

HAUSA

Kasar Sin ta baiwa Somaliya gudummawar alluran rigakafin COVID-19 na kamfanin Sinopharm

2021-12-06 09:51:06 CRI

Kasar Sin ta baiwa Somaliya gudummawar alluran rigakafin COVID-19 na kamfanin Sinopharm_fororder_Ibrahim1

Jiya ne, kasar Somaliya ta karbi gudummawar alluran rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin Sinopharm guda 500,000 daga kasar Sin, don taimakawa karfafa yaki da cutar a cikin kasar a yayin da ake fama da nau'in cutar na Omicron.

Jakadan kasar Sin a Somaliya Fei Shengchao, ya ce zuwan allurar rigakafin na COVID-19, ya nuna aniyar kasar Sin na mutunta alkawuran da ta dauka a zahiri da kuma kare rayuka da lafiyar al'ummar Somaliya.

Fei ya ce, kasar Sin za ta yi aiki tare da Somaliya wajen yaki da cutar, da zurfafa hadin gwiwa a fannin likitanci da kiwon lafiya, da kare rayuwa, da kimar kowane mutum, da daukar sabon salo na gina al'ummar Sin da Afirka mai makomar bai daya a sabon zamani..

A nata jawabin, ministar lafiya da ayyukan jin kai ta kasar Somaliya Fawziya Abikar Nur, ta yabawa gwamnatin kasar Sin da gudummawar rigakafin. Tana mai cewa, alluran na Sinopharm sun zo a kan lokaci, ganin yadda a cewarta sabon nau'in Omicron ke yaduwa cikin sauri.

Somaliya, wacce ta kaddamar da shirin yiwa ’yan kasarta allurar rigakafin cutar a ranar 16 ga Maris, ta samu gudummawar allurai 200,000 na kamfanin Sinopharm daga kasar Sin a ranar 11 ga Afrilu don bunkasa yaki da cutar ta COVID-19. (Ibrahim)