Aliyu Lantewa: Ina kira ga matasan Najeriya su yi karatu su taimaki kasarsu
2021-12-06 11:09:09 CRI
Aliyu Lantewa, wani dalibi dan asalin jihar Yoben tarayyar Najeriya ne, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na biyu a jami’ar nazarin harkokin man fetur ta kasar Sin dake yankin Changping na birnin Beijing. A zantawar da ya yi da Murtala Zhang, Aliyu Lantewa ya ce dalilin da ya sa ya zabi ya karanci ilimin man fetur shi ne domin bada gudummawarsa ga inganta harkokin man fetur a gida Najeriya, ganin yadda Allah ya horewa kasar dimbin albarkatun mai din.
Malam Aliyu ya kuma yi kira ga matasan Najeriya, da su rungumi karatu, saboda a cewarsa, hakan zai ba su damar taimakawa kansu da kasarsu baki daya. (Murtala Zhang)