logo

HAUSA

An sake zabar Adama Barrow a matsayin shugaban kasar Gambia

2021-12-06 11:21:41 CRI

An sake zabar Adama Barrow a matsayin shugaban kasar Gambia_fororder_211206-Adama Barrow-Ahmad

Shugaban hukumar zaben kasar Gambiya IEC, Alieu Momar Njie, a jiya Lahadi ya ayyana Adama Barrow, jagoran jam’iyyar NPP, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Asabar.

Barrow ya samu jimillar kuri’u 457,519, wanda ya samu kusan kashi 53 bisa 100 na yawan kuri’un da aka kada a zaben. Ya yi galaba kan babban abokin takararsa Ousainu Darboe, na jam’iyyar UDP, wanda ya samu kuri’u 238,253.

A shekarar 2016 aka zabi Barrow a karon farko a matsayin shugaban kasar Gambia karkashin hadakar kawancen jam’iyyun adawa bakwai har ma da ’yan takarar indifenda, inda ya kada tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh. Tun daga wancan lokacin Jammeh yake gudun hijira a kasar Equatorial Guinea.

Gabanin zaben nasa, a lokacin gangamin yakin neman zabensa, Barrow ya yi alkawarin inganta fannin noma da bunkasa samar da kayayyakin more rayuwa a kasar. (Ahmad)