logo

HAUSA

Shugaban jamhuriyar Kongo ya gana da babban jami’in diflomasiyyar Sin

2021-12-06 10:03:24 CRI

Shugaban jamhuriyar Kongo ya gana da babban jami’in diflomasiyyar Sin_fororder_211206-Ahmad-Yang Jiechi

Shugaban kasar jamhuriyar Kongo, Denis Sassou Nguesso, a ranar Lahadi ya gana da Yang Jiechi, mamban hukumar siyasa na kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, kana daraktan ofishin hulda da kasashen waje na kwamitin tsakiyar CPC.

Yang ya ce, kasar Sin za ta yi amfani da damar aiwatar da sakamakon da aka samu na taron ministocin dandalin FOCAC karo na takwas don ci gaba da taimakawa jamhuriyar Kongo a yaki da annobar COVID-19, da kara lalibo sabbin hanyoyin zurfafa hadin gwiwa, da daga matsayin hadin gwiwarsu a fannoni daban daban, da suka hada da samar da kayayyakin more rayuwa da kafa yankin masana’antu, domin bayar da babbar gudunmawar bunkasar tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar al’ummar jamhuriyar Kongo.

Yang ya ce, a matsayinsu na kasashe masu tasowa, Sin da jamhuriyar Kongo sun cimma matsaya kan muhimman batutuwan kasa da kasa, ya kara da cewa, bangarorin biyu za su kara zurfafa hadin gwiwarsu, da daga matsayin gina kyakkyawar makomar al’ummun Sin da Afrika a sabon zamani, da hadin gwiwa wajen nuna adawa da ra’ayin bangare guda, da kiyaye hakikanin tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban, da tabbatar da daidaito da adalci a harkokin kasa da kasa da kuma kokarin tabbatar da moriyar bai daya na kasashe masu tasowa.

A nasa bangaren shugaban kasar Kongo ya ce, jamhuriyar Kongo a shirye take ta karfafa hadin gwiwa da bangaren kasar Sin kan al’amurran dake shafar MDD da batutuwan shiyya na Afrika, da nuna adawa da ra’ayin bangare guda, da goyon bayan hadin gwiwar bangarori daban daban, da hadin gwiwar tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Afrika da duniya baki daya. (Ahmad)