logo

HAUSA

Amurka tana fakewa da maganar dimokuradiya don tsoma baki cikin harkokin gidan sauran sassa

2021-12-06 19:04:54 CRI

Kakakin gwamnatin jihar Xinjiang ta kasar Sin Xu Guixiang, ya furta cewa, jama’ar kasar Sin sun cimma wata babbar nasara wajen kirkiro tsarin dimokuradiya da ya shafi dukkan matakan ayyukan na kasar.

Xu ya fadi hakan ne, yayin da yake jagorantar wani taron manema labaru da ya shafi batun jiharsa, a birnin Beijing, inda aka gabatar da mafi yawan bayanai kan batun dimokuradiya. A cewar jami’in, jihar Xinjiang ta tsaya kan manufar maida cikakken hankali a kokarin kare moriyar jama’a, da aiwatar da tsarin dimokuradiya da ya shafi dukkan matakan ayyuka, da kokarin kyautata harkokin siyasa irin na dimokuradiya karkashin tsarin siyasar gurguzu, ta yadda aka samu tabbatar da ikon al’ummun kabilu daban daban, na yanke shawara kan harkokin siyasar jihar.

Jami’in ya kara da cewa, wasu Amurkawa, da wasu al’ummun kasashen yamma, da suke kin jinin kasar Sin, sun shafa bakin fenti ga tsarin dimokuradiya na Xinjiang, gami da neman tsoma baki cikin harkokin jihar, da na kasar Sin baki daya. Saboda haka, sam ba za a yi hakuri da mumumman ayyukan da suke yi ba.

Ya ce kullum kasar Amurka na neman fakewa da batun dimokuradiya, don yin shisshigi cikin harkokin cikin gida na sauran sassa, amma a hakika sam ba ta da ikon yin magana kan batun dimokuradiyar sauran kasashe da yankuna. (Bello Wang)