logo

HAUSA

Menene Hakikanin Salon Dimokaradiyyar Kasar Sin?

2021-12-06 20:19:33 CRI

Menene Hakikanin Salon Dimokaradiyyar Kasar Sin?_fororder_微信图片_20211206201838

Demokaradiyya dai wani tsari ne na shugabancin al’umma da tafiyar da jagorancin kasa, ko da yake ma’anar demokaradiyya da manufarta ya dogara ne da yadda mahukunta kowace kasa ke gudanar da kasar ta yadda zai dace da yahayin tarihi, al’adu, tattalin arziki, da yanayin zaman rayuwar al’umma, kuma bisa dacewa da yanayin da kasar ke ciki. Wannan yana daga cikin manyan dalilan da kasar Sin ke kara ayyana matsayarta game da shin ko menene hakikanin manufar demokaradiyya a mahangar kasar? Ko tsarin demokaradiyyar kasar Sin ya dace da yanayin kasar da kuma al’ummarta? Sannan ko kwalliya tana biyan kudin sabulu karkashin tsarin demokaradiyyar kasar Sin? Amsoshin wadannan muhimman tambayoyi za su fayyace menene hakikanin ma’anar demokaradiyyar kasar Sin. A karshen wannan mako, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fidda takardar bayani mai taken “Dimokaradiyyar Kasar Sin.” Takardar ta yi nuni da cewa, dimokaradiyyar kasar Sin, dimokaradiyya ce ta al’umma, wato al’umma ne jigo da ginshikin harkokin kasar. Kana dimokradiyya hakki ne na al’ummomin duk wata kasa, ba hakki ne na wasu kasashe na musamman ba. A don haka, al’ummun kasa ne ya dace su tantance yadda ake bin tafarkin dimokaradiyya a kasar. Abun nufi, bai kamata wasu kasashe su yi korafi ba, ko kasa tana bin tafarkin dimokaradiyya, ko a’a, kasa da kasa ne ya dace su tantance, ba wai wasu ‘yan tsirarun kasashe su rika shisshigi ba. Akwai mabambantan hanyoyi da ake bi domin tafiyar da harkokin dimokaradiyya. Don haka, bai kamata a yi amfani da mizani daya don tantance mabambantan tsare-tsaren siyasa da al’adun siyasa iri-iri na duniya ba, domin yin hakan, ba shi ne ainihin dimokaradiyya ba. Ko shakka babu, yadda ma’anar dimokaradiyya take ga kasar Sin da al’ummar Sinawa ya yi hannun riga da yadda wasu kasashen yammacin duniya ke ikirarin su ne kanwa uwar gami wajen kafa tsarin dimokaradiyyar duniya. Koda a karshen wannan mako, wannan batu ya yi matukar daukar hankalin duniya, alal misali, shafin intanet na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya fidda wani rahoto mai taken, “Matsayin demokaradiyya a Amurka." Bisa dogaro da hujjoji da kuma ra’ayoyin masana, rahoton ya bankado gazawa da yin karan zaye ga demokaradiyya a kasar Amurka da kuma hadarin dake tattare da yada irin wannan demokaradiyyar zuwa ga sauran kasashen duniya. Rahoton dai ya nemi Amurka ta yi kokarin inganta tsarinta, da irin salon da take amfani dashi a tsarin dimokardiyya, kana ta sauya hanyar mu’amalarta da sauran kasashen duniya. Rahoton ya ce, ita dai dimokaradiyya batu ne na muradun bai daya na dukkan bil adama. Hakki ne na dukkan kasashen duniya, ba wai ya kebanta ne ga wasu ‘yan tsiraru ba, demokaradiyya tana iya daukar salo iri daban daban, kuma babu wani batu na cewa tsarin wani bangare shi ne yafi dacewa sama da na kowa. Sam-sam ba tsarin demokaradiyya ba ne a auna salon demokaradiyyar sauran kasashen duniya da wani tsari guda daya tilo ko kuma a kwatanta tsarin siyasar kasashe daban daban da wani tsari daya tak ko mahangar wani bangare daya. Ko shakka babu, dimokaradiyyar kasar Sin, dimokaradiyya ce ta al’umma, wato al’umma su ne jigo da ginshikin harkokin kasar. Kana dimokradiyya hakki ne na al’ummomin duk wata kasa, ba hakki ne na wasu kasashe na musamman ba. Da ma dai gwamnatin kasar Sin ta sha bayyana aniyarta na mayar da rayuwar jama’a a gaban komai, sabanin masu yin ikirarin kafa demokaradiyya amma suna keta hakkokin bil adama babu gaira babu dalili.(Ahmad Fagam)