Al’ummun kasashen duniya sun fahimci illolin demokuradiyya mai salon Amurka
2021-12-05 21:38:19 CRI
Yau Lahadi 5 ga wata, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da rahoton “Matsayin demokuradiyya na Amurka”, inda aka bayyana cewa, “Tsarin demokuradiyya na kasar Amurka sakamako ne da Amurka ita kanta ta samu bayan kokarin da ta yi, yana da halayyar musamman, bai kamata a yada shi a sauran kasashen duniya ba, kana bai kamata a mayar da shi tsari na gari ba.”
Rahoton ya yi cikakken bayani game da illolin da tsarin demokuradiyyar Amurka ke haifarwa, an lura cewa, demokuradiyya mai salon Amurka ta gamu da matsala mai tsanani, lamarin da ya sa “taron kolin demokuradiyya” da Amurka za ta kira ya kasance tamkar abin wasa.
Sakamakon binciken da CNN ta gudanar kan ra’ayin jama’a a watan Satumban da ya gabata ya nuna cewa, Amurkawa kaso 56 bisa dari suna ganin cewa, demokuradiyyar Amurka tana gamuwa da hari, binciken da cibiyar nazari ta Pew ta yi a bana shi ma ya bayyana cewa, Amurkawa kaso 72 bisa dari sun dauka cewa, Amurka wadda take kiran kanta da sunan “madubin demokuradiyya” ba za ta kasance abin koyi ga sauran kasashe a bangaren tsarin demokuradiyya ba. A bayyane an lura cewa, al’ummun kasa da kasa su ma sun yi matukar fahimtar illolin demokuradiyya mai salon Amurka.(Jamila)