logo

HAUSA

An kammala zaben shugaban kasar Gambiya yayin da ‘yan takara ke kiran jama’a su zauna lafiya

2021-12-05 15:20:10 CRI

Da misalin karfe 5 na yammacin ranar Asabar, aka kammala jefa kuri’u a Banjul, babban birnin kasar Gambiya, inda shugaban kasar da sauran ‘yan takarar neman shugabancin kasar ke ci gaba da yin kira ga al’ummar kasar da su zauna lafiya.

Wannan ne karon farko da aka gudanar da zaben shugaban kasa a Gambiya, tun bayan zaben da ya gudana a shekarar 2016, inda shugaban kasar mai ci ya kada Yahya Jammeh, tsohon shugaban kasar da ya shafe shekaru da dama yana jan ragamar shugabancin kasar.

A ranar Asabar, dubun dubatar jama’a sun yi fitar dango domin zabar shugaban kasa daga cikin ‘yan takara shida dake fafatawa a zaben. Shugaban kasar mai ci Adama Barrow, na jam’iyyar NPP mai mulkin yana fuskantar zazzafar adawa daga tsohon mataimakinsa Ousainou Darboe, wanda ke takara karkashin jam’iyyar United Democratic Party (UDP).

Jim kadan bayan jefa kuri’arsa a rumfar zabe ta filin McCarthy dake birnin Banjul, shugaba Adama Barrow, ya yabawa jama’ar Gambiya bisa yadda suka yi fitar dango don kada kuri’unsu.

Ya kuma shawarci hukumar zaben kasar (IEC) da ta yi adalci, domin hakan ne zai sa dukkan jama’ar kasar su amince da sakamakon zaben.(Ahmad)