logo

HAUSA

Putin da Biden za su tattauna ta kafar bidiyo a ranar Talata

2021-12-05 15:30:30 CRI

Putin da Biden za su tattauna ta kafar bidiyo a ranar Talata_fororder_putin

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da takwaransa na Amurka Joe Biden, za su tattauna ta kafar bidiyo a ranar Talata mai zuwa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na RIA Novosti ya ba da rahoto, inda ya jiyo kakakin fadar Kremlin, Dmitry Peskov ya bayyana hakan.

A cewar Peskov, shugabannin biyu za su yi tattaunawar ne da yammacin ranar Talata.

Da aka tambaye shi game da tsawon lokacin da tattaunawar za ta dauka, kakakin ya ce, shugabannin kasashen ne kadai ke da ikon yanke hukunci kan tsawon lokacin da za su shafe yayin tattaunawar.

Sai dai rahotanni sun ce, ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna batun dake shafar kasar Ukraine da sauran batutuwa da dama.(Ahmad)