logo

HAUSA

Kwamitin sulhun MDD ya sake tsawaita wa’adin yaki da ‘yan fashin teku a Somaliya

2021-12-05 16:50:17 CRI

Kwamitin sulhun MDD ya sake tsawaita wa’adin yaki da ‘yan fashin teku a Somaliya_fororder_hoto1

A ranar 3 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2608, inda ya tsawaita wa’adin aikin hadin gwiwar kasashen duniya da kungiyoyin yankin da gwamnatin kasar Somaliya don yakar ‘yan fashin teku na tsawon watanni 3.

Bisa wannan kuduri, za a gudanar da bincike tare da gurfanar da wadanda suka goyi bayan ‘yan fashin tekun Somaliya a gaban kotu. An kuma sa kaimi ga gwamnatin kasar Somaliya don ta kafa tsarin yin sintiri a yankunan dake kewayen tekun, domin yin rigakafi da hana aikace-aikacen ‘yan fashin tekun.

Haka kuma, kwamitin sulhu na MDD ya sake yin kira ga kasashen duniya da kungiyoyin yankin da su shimfida jiragen ruwan sojojin teku, da makamai, da jiragen saman soja domin yaki da ‘yan fashin tekun, inda ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwar gamayyar kasa da kasa kan wannan aiki.

Bisa sabon rahoton babban magatakardan MDD game da batun ‘yan fashin tekun Somaliya da aka fidda, an ce, daga shekarar 2011 zuwa yanzu, aikace-aikacen fashi sun ragu bisa kokarin da aka bayar wajen yaki da ‘yan fashin tekun cikin hadin gwiwa, amma, ana ci gaba da fuskantar karin kalubaloli a bangaren. (Maryam)