logo

HAUSA

Masanin Kenya: Kasancewar Sin a WTO tsawon shekaru 20 ya taimaka wa kasashen Afirka sosai

2021-12-05 16:53:47 CRI

Masanin Kenya: Kasancewar Sin a WTO tsawon shekaru 20 ya taimaka wa kasashen Afirka sosai_fororder_hoto2

Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 20 da kasancewar kasar Sin a kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO. Dangane da wannan batu, masanin kasar Kenya Cavins Adhill ya ce, cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta ba da gudummawar kashi 20 bisa dari cikin karuwar tattalin arzikin kasashen Afirka. Kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen kare tsarin ciniki a tsakanin sassa daban daban, lamarin da ya zama abin koyi ga sauran kasashe maso tasowa. A matsayin mambar kungiyar WTO, kasashe da dama suna koyon fasahohin kasar Sin, domin neman ci gaba ta hanyoyi masu dacewa da kuma bisa tsarin kungiyar WTO.

Daga shekarar 2000 zuwa yanzu, yawan hajojin da kasar Sin ta shigo da su daga kasashen Afirka ya kai na dalar Amurka triliyan 1.2, yayin da ta fitar da hajoji na dalar Amurka triliyan 1.27 zuwa kasashen Afirka. Cikin ‘yan shekarun nan kuma, jimllar ciniki dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ya kai dalar Amurka biliyan 200 cikin ko wace shekara, kuma, adadin amfanin gona da kasar Sin ta shigo da su daga kasashen Afirka yana karuwa cikin sauri, har matsakacin karuwar adadin cikin shekaru 5 da suka gabata, ya kai kashi 11.4 bisa dari.

Dangane da wannan batu, Cavins Adhill ya ce, kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen kare tsarin cinikin dake tsakanin bangarori daban daban, lamarin da ya goyi bayan kasashen Afirka wajen neman bunkasuwa da kansu. Hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka bisa tsarin cinikin dake tsakanin bangarori daban daban, zai taimakawa kasashen Afirka a fannin yin kwaskwarimar tattalin arziki. (Maryam)