logo

HAUSA

An kashe mutane 31 a wani hari a tsakiyar Mali

2021-12-05 16:39:32 CRI

A kalla mutane 31 aka kashe yayin da wasu 17 suka samu raunuka bayan da wasu ‘yan bindiga suka kaddamar da hari a ranar Juma’a kan wata babbar mota dake dauke da fararen hula a tsakiyar kasar Mali, hukumomin kasar sun bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Sanarwar, wacce gwamnatin rikon kwaryar Mali ta fidda, ta bayyana cewa, wasu gungun ‘yan bindiga dauke da makamai ne suka kaddamar da harin tare da cinna wuta kan babbar motar dake makare da mutane yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani yanki dake kusa da kauyen Songho.

A cewar sanarwar, tuni aka tura tawagar jami’an tsaro zuwa yankin don gano mutanen dake da alhakin kai harin, tare da yin alkawarin daukar matakan hukunta wadanda suka shirya mummunan harin.

Shugaban kasar Mali na rikon kwarya Assimi Goita, ya ayyana makoki na kwanaki uku a duk fadin kasar wanda ya fara tun daga yau Lahadi domin nuna alhini ga mutanen da harin ya rutsa da su.(Ahmad)