logo

HAUSA

Shugaban CMG: Ko Amurkawan da ‘yan sanda suka kashe sun ji dadin demokuradiyyar kasarsu?

2021-12-05 21:35:13 CRI

Shugaban CMG: Ko Amurkawan da ‘yan sanda suka kashe sun ji dadin demokuradiyyar kasarsu?_fororder_shen

Tsarin demokaradiyya yana cike da tarihin kasa da al’adu gami da yanayin zaman rayuwar al’umma, don haka, babu wani tsari da za a iya bayyana shi a matsayin salon demokaradiyya da ya fi na kowace kasa.

Shen Haixiong, shugaban CMG na kasar Sin ya yi wannan tsokaci a taron dandalin demokaradiyya na kasa da kasa: wanda ke shafar muradun bil adama wanda aka kaddamar a ranar Asabar.

A cikin jawabinsa, ya zayyana wasu munanan sakamako wanda yunkurin Amurka na tilasta bin salon manufar demokaradiyyarta ta hanyar amfani da karfin tuwo ya haifar, inda ya bayyana cewa, manufar Amurkar dake tutiyar zama jagorar kafa tsarin demokaradiyya a duniya ya ci tura, kuma a bayyane take salon demokaradiyyar Amurka ya gamu da tazgaro, kuma yana cikin wani halin jinya mai tsananin gaske.

Shen ya kuma nanata cewa: idan aka yi la’akari da yadda mummunan halin kuncin da jama’ar kasar Afghanistan suka shiga wadanda sojojin Amurka suka kashe karkashin abin da Amurkar ke ikirari wai hare hare ta jirage marasa matuka, na jima ina tunani shin wannan shi ne abin da Amurka take kira a matsayin demokaradiyya? Ko Amurkawan da ‘yan sanda suka kashe sun ji dadin demokuradiyyar kasarsu?(Mai fassarawa: Ahmad daga CRI Hausa)