logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya jaddada bukatar raya harkokin addini a kasar

2021-12-04 20:41:36 CRI

Shugaban kasar Sin ya jaddada bukatar raya harkokin addini a kasar_fororder_Z]){~8@(ZYLJ~]004R65W1F

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya nanata bukatar daukaka akidar raya harkokin addini a kasar da bada jagoranci mai inganci wajen rungumar addinai a cikin al’ummar gurguzu.

Xi Jinping wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS kuma shugaban rundunar sojin kasar, ya bayyana haka ne da yake jawabi ga babban taron kasa kan ayyukan dake da nasaba da harkokin addini da aka yi daga jiya Jumma’a zuwa yau Asabar a nan birnin Beijing. (Fa’iza Mustapha)