logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da takardar bayani kan dimokaradiyyarta

2021-12-04 11:01:16 CRI

Kasar Sin ta fitar da takardar bayani kan dimokaradiyyarta_fororder_AA

Ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da wata takardar bayani mai suna “Dimokaradiyyar Kasar Sin” a yau Asabar, inda ya shirya taron manema labarai don bayyana abubuwan dake cikin takardar.

Takardar ta yi nuni da cewa, dimokaradiyyar kasar Sin, dimokaradiyya ce ta al’umma, wato al’umma ne jigo da ginshikin harkokin kasar. Kana dimokradiyya hakki ne na al’ummomin duk wata kasa, ba hakki ne na wasu kasashe na musamman ba. A don haka, al’ummomin kasa ne ya dace su tantance yadda ake bin tafarkin dimokaradiyya a kasar. Abun nufi, bai kamata wasu kasashe su yi korafi ba. Ko kasa tana bin tafarkin dimokaradiyya, ko a’a, kasa da kasa ne ya kamata su tantance, ba wai wasu  kasashe kalilan su rika shishigi ba. Akwai mabambantan hanyoyi da ake bi domin tafiyar da harkokin dimokaradiyya. Saboda haka, bai kamata a yi amfani da mizani daya don tantance mabambantan tsare-tsaren siyasa da al’adun siyasa iri-iri na duniya ba, domin yin hakan, ba ainihin dimokaradiyya ba ne. (Murtala Zhang)