logo

HAUSA

Tsohon dan wasan damben boxing na Zimbabwe na kokarin yaye sabbin rukunin ‘yan dambe

2021-12-04 16:15:00 CRI

Tsohon dan wasan damben boxing na Zimbabwe na kokarin yaye sabbin rukunin ‘yan dambe_fororder_1202-boxing

Ana iya ganin yara kanana 2 sanye da safar boxing suna kaiwa juna naushi akai akai, gaban ‘yan kallo dake shewa. Duk da karancin shekarun su, suna nuna matukar sha’awar zama taurarin ‘yan damben boxing na duniya.

Wadannan yara dai ‘yan asalin Mbare ne, wani yanki mai tarin matalauta dake yankin wajen birnin Harare, fadar mulkin kasar Zimbabwe.

Mai horas da su damben Zvenyika Arifonso, wanda ya taba lashe gasar Boxing ta kasashe renon Ingila, ta hanyar horas da yara kanana daga yankuna matalauta wannan wasa, yana fatan samar da wani rukuni na ‘yan damben boxing da za su yi fice a duniya.

Koci Arifonso, wanda akan kira da "Mosquito" wato sauro a harshen hausa, sakamakon yanayin rashin kibar sa, ya horas da ‘yan wasan damben boxing da dama a kasar Zimbabwe.

Da yake tsokaci game da hakan, Arifonso ya ce "Akwai ‘yan wasan boxing da dama da suka koyi wasan daga gare shi, wadanda kuma a yanzu ke dogaro da kan su, suna cin moriyar wasan.

Daya daga irin wadannan dalibai na sa shi ne Antony Mapako mai shekaru 24 da haihuwa, wanda a yanzu ke ta kokarin zama tamkar kocin sa a fagen wannan Boxing.

Yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Antony Mapako ya ce "A matsayi na na dan wasan boxing, ina fatan nan da shekaru 5 masu zuwa, zan daga tutar kasar Zimbabwe kamar yadda Mosquito ya taba yi a baya”.

A shekarar 1998, Arifonso ya doke Paul Weir na kasar Scotland, ya kuma lashe kambin Boxing na gasar kasashe renon Ingila da aka gudanar a birnin Glasgow.

To sai dai kuma, duk da nasarorin da ya cimma yana da karancin shekaru, a yau Arifonso ba shi da wasu fa’idoji masu yawa da suka wanzu tare da shi, samakon nasarorin na baya. Amma duk da haka, ya ci gaba da kokarin sa na ganin ya yaye ‘yan wasan Boxing da za su kai matsayin koli a matakin kasa da kasa daga Zimbabwe.

Duk da cewa a ganin wasu ana koyon wasan Boxing ne domin kawar da hankalin yara daga fadawa rigingimu a lokacin kuruciya, a wasu lokuta hakan ba ta samuwa. Sai dai duk da haka Arifonso na da ra’ayin cewa, wasa irin na fada kamar Boxing, na iya koyawa yara da’a da aiki tare da sauran mutane.

Mapako ya kara da cewa, Boxing na iya zama hanyar baiwa matasa dama ta samun nishadi, da kawar da kan su daga shiga tashe tashen hankula ko fadace fadace. Ya ce "Shiga wasan Boxing na samar da damar yin horo da kare martabar kai, saboda ta hakan muna iya koyarda yara hanyoyin zaman lafiya tare da sauran al’umma. Muna koyawa yara hanyar samun martaba da mutunci daga al’umma, ba wai koyar da fada da sauran mutane ba ne".

Baya ga koyar da da’a da karfafa zuciyar yara, Arifonso ya ce wasan na kawar da matasa daga shiga miyagun dabi’u da suka zama ruwan dare tsakanin al’umma.

Rashin ababen more rayuwa ga matasa a unguwannin matalauta kamar unguwar Mbare, na nufin yara na da lokaci mai yawa na zaman kashe wando, wanda hakan ke sa su yi ta’ammali da miyagun abokai.

Mapako ya ce "Wannan wasa hanya ce ta kare yara daga muggan abokai da munanan ayyuka, ko aikata laifuka, da sauran su, saboda yaran na da abun yi dake cike musu lokaci. Idan sun gaji ba bu sauran abun yi sai bacci”.

A matsayin sa na yanki mai fama da fatara a birnin Harare, mai kuma fama da aikata laifuka, da shan miyagun kwayoyi da karuwanci, wuri ne dake haifar da lalacewar rayukan matasa da dama.

Mapako ya ce "Yara na rasa rayukan su, suna shiga shaye shaye, wasu na shiga karuwanci, wasu ma suna zama ‘yan shaye shaye, wasu kuma su zama barayi".

A bangaren ‘yan mata, Tinotenda Mazuru mai shekaru 15 da haihuwa, ta kamu da sha’awar wasan Boxing, wanda hakan ya kawar mata da tunanin banbancin jinsi.

Game da hakan, Tinotenda Mazuru ta ce "Ina yin wannan wasa ne saboda na zama kwararriyar ‘yar Boxing, kuma ina fatan nunawa mutane cewa mata ma za su iya yin fice a duniya. Kaza lika koyon kare kai na kara sanyawa mata sha’awar wasan. Yana ba wa mata horon kyautata dabi’a, da dakile nuna banbanci da ake nuna musu”.

Duk da cewa ana kallon wasan Boxing a matsayin abun dake samarwa matasa abun yi maimakon zaman banza, batun daukar nauyin wasan a Zimbabwe na ci gaba da zama babban kalubale, wanda hakan ke sanya masu sha’awar zama kwararrun ‘yan Boxing, neman wata sana’ar ta daban domin samun abun rike kan su.