An cimma burin Sin da Laos ta hanyar shimfida layin dogo a tsakaninsu
2021-12-04 16:24:34 CRI
Shugabannin Sin da Laos, sun bada umurnin kaddamar da layin dogo tsakanin kasashen biyu a hukunce, jiya Jumma’a, ta kafar bidiyo.
Kafin hakan, layin dogo daya, mai tsawon kilomita 3.5 ne kadai ke akwai a cikin kasar Laos, wanda ya hada kasar da Thailand. Bayan shekaru 5 da gina shi, yanzu an kaddamar da layin dogo tsakanin Sin da Laos mai tsawon kilomita 1035, wanda zai rage lokacin zirga-zirgar jiragen kasa tsakanin babban birnin kasar Laos da iyakar kasar dake tsakaninta da Sin, daga kwanaki biyu zuwa awoyi uku, wato idan aka tashi daga babban birnin Laos zuwa birnin Kunming na kasar Sin. Wannan ya sa kasar Laos shiga lokacin amfani da jiragen kasa mai sauri.
Ban da samar da sauki ga zirga-zirga tsakanin kasashen biyu, layin dogon zai sa kaimi ga bunkasa sha’anin yawon shakatawa, da aikin noma, da albarkatun ruwa, da raya birane, da kuma gina yankunan tattalin arziki. Wannan layin dogo ya zama tamkar hanya mai samar da kyakkyawar makoma. Tun daga lokacin da aka fara gina shi a shekarar 2016, mutane fiye da dubu 5 a kasar Laos sun shiga aikin. Matasan kasar Laos da dama, sun fita daga yankunan duwatsu, sun bude idanunsu, da kuma fahimtar kimiyya da fasaha na zamani.
A nan gaba, shawarar “ziri daya da hanya daya” za ta taimakawa karin mutane, su bude idanunsu. Wannan ya shaida dalilin da ya sa Sin ta bayar da wannan shawara, wato sa kaimi ga samun ci gaba tare, da kara amfanawa jama’a. (Zainab)