Masana sun bada ra’ayoyi kan tattalin arzikin kasar Sin da bada ilmi da sauransu
2021-12-04 20:35:20 CRI
Daga ranar 1 zuwa 4 ga watan nan, an yi taron kasa da kasa game da “Fahimtar Kasar Sin” na shekara ta 2021, mai taken “Daga ina aka fito, ina kuma aka dosa—— Sauye-sauyen duniya a shekaru 100 na kasar Sin, gami da jam’iyyar kwaminis ta kasar” a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin.
Masanan da suka halarci taron sun tattauna da wakilan babban gidan rediyo da telebiji na kasar Sin wato CMG, inda suka bayyana ra’ayoyinsu kan tattalin arziki da tsarin ilimi na Sin, da sauransu.