logo

HAUSA

Afrika na matse kaimi wajen gano nau’in Omicron yayin da masu kamuwa da COVID-19 ke karuwa a kudancin nahiyar

2021-12-03 11:12:31 cri

Afrika na matse kaimi wajen gano nau’in Omicron yayin da masu kamuwa da COVID-19 ke karuwa a kudancin nahiyar_fororder_src=http___n.sinaimg.cn_sinakd20211130s_100_w1024h676_20211130_e669-79aab9349bf3f71083e6d6f0f5ca16b4&refer=http___n.sinaimg

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, kasashen Afrika na matse kaimi wajen daukar matakan ganowa da takaita yaduwar nau’in Omicron na cutar COVID-19, yayin da adadin sabbin masu kamuwa da cutar ke karuwa da kaso 54 saboda barkewarta a kudancin Afrika.

Ofishin WHO a nahiyar Afrika dake Brazaville na Congo, ya bayyana cewa, an gano nau’in na Omicron a kasashe 4 da suka hada da Botswana da Afrika ta Kudu da Ghana da Nigeria, yayin da kawo yanzu, aka gano sabon nau’in cutar a kasashe fiye da 20. A cewar ofishin, Botswana da Afrika ta kudu ne ke da kaso 62 na adadin wadanda suka kamu da nau’in Omicron a duniya.

Daraktar ofishin WHO a nahiyar Afrika, Matshidiso Moeti, ta yi gargadin cewa, gaggawar gano nau’in cutar da bada rahoton bullarta da Botswana da Afrika ta Kudu suka yi, ya samarwa duniya lokacin shiryawa tunkararta. Ta ce ya kamata a gaggauta amfani da damar da ake da ita wajen inganta matakan ganowa da na kariya. Tana mai kira ga kasashen Afrika su yi wa matakansu na tunkarar cutar garambawul domin dakile bazuwarta a nahiyar.

Ta kara da cewa rashin adadi mai yawa na wadanda aka yi wa riga kafi, da ci gaba da yaduwar cutar, da sauyawar yanayin cutar, abubuwa ne masu hadari. Haka kuma, nau’in na Omicron ya tabbatarwa duniya cewa barazanar COVID-19 gaskiya ce. Ta ce idan aka inganta samar da alluran riga kafi, kasashen Afrika za su fadada aikin bayar da alluran, domin samun adadin mai yawa na al’ummar dake da kariya. (Fa’iza Mustapha)