Waiwaye Ado Tafiya
2021-12-03 16:49:21 CRI
Muna farin cikin sanar da ku cewa, yau ne kasar Sin ta cika shekaru 80 da fara watsa shirye-shiryen rediyo ga kasashen ketare. A ranar 3 ga watan Disamban shekarar 1941 wato shekaru 80 da suka gabata, kasar Sin ta fara gabatar da shirye-shiryen rediyo da harshen Japananci, wannan ya sa aka ayyana ranar a matsayin ranar da kasar ta fara watsa shirye-shiryen rediyo ga kasashen ketare. Har ila yau, a wannan shekara ta 2021 ne kasar Sin ta cika shekaru 58 da fara watsa shirye-shiryen rediyo da harshen Hausa. Hausawa kan ce, waiwaye adon tafiya, don haka, cikin shirinmu na yau, za mu waiwayi tarihin sashen Hausa tare da wasu tsoffin maaikatan sashen.(Lubabatu)