logo

HAUSA

Wata kafar Jamus ta hakaito mahangar wani masani dan kasar Singapore game da tunanin kasashen yamma don gane da Sin

2021-12-03 15:11:57 cri

Wata kafar Jamus ta hakaito mahangar wani masani dan kasar Singapore game da tunanin kasashen yamma don gane da Sin_fororder_微信图片_20211203150551

Kafar watsa labarai ta yanar gizo ta kasar Jamus mai suna “Die Welt”, ta hakaito mahangar tsohon wakilin dindindin na Singapore a MDD Kishore Mahbubani, wanda ke cewa babbar matsalar da dama daga kasashen yamma ita ce, ba su da cikakkiyar fahimtar kasar Sin.

Mr. Kishore Mahbubani, ya ce al’ummar Sinawa na da irin na su tarihin salon siyasa, da al’adun gargajiya na musamman. Kuma sun san abubuwan da ka iya yiwuwa da wadanda ba za su yiwu ba a kasar su.

Kaza lika shaidu sun tabbatar da cewa, a halin yanzu, mafiya yawan Sinawa na cike da farin ciki sama da halin da suke ciki a baya.  (Saminu)