logo

HAUSA

Sin da Afrika sun yi alkawarin karfafa hadin gwiwarsu don yaki da sauyin yanayi

2021-12-02 10:30:10 CRI

Sin da Afrika sun yi alkawarin karfafa hadin gwiwarsu don yaki da sauyin yanayi_fororder_sauyin yanayi

Kasashen Sin da Afrika sun fidda yarjejeniyar hadin gwiwar yaki da matsalolin sauyin yanayi, bayan sun lura cewa matsalar sauyin yanayi ta kasance a matsayin wani babban kalubale dake barazana ga muhallin halittu, da zaman rayuwar al’umma, da kuma bunkasuwar tattalin arzikin kasashen na Sin da Afrika.

Dukkan bangarorin biyu sun amince da shawarwari da kuma babbar gudunmawar da kasar Sin ta bayar, a matsayinta da kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kuma Afrika, a matsayinta na nahiyar dake da kasashe masu tasowa mafi yawa a duniya, hadin gwiwa da kuma daukar matakan yaki da sauyin yanayi su ne abubuwa mafiya dacewa, kamar yadda sanarwa yarjejeniyar ta bayyana.

A cewar sanarwar, shawo kan matsalolin sauyin yanayi da yadda ake samun karuwar kwararar bakin haure ya kasance a matsayin wani kalubale dake damun dukkan bil adama, dukkan bangarorin Sin da Afrika sun bukaci kasashen duniya su yi aiki tare karkashin tsarin hadin gwiwar bangarori daban daban.

Ya kamata kasashen da suka ci gaba su yi kokarin gaggauta cika alkawurransu na samar da kudaden tallafawa kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afrika, domin su iya jure matsalolin sauyin yanayi, da kuma yin kokarin cike gibi ta hanyar alkawarin tara dala biliyan 100 a duk shekara tun daga shekarar 2020, in ji sanarwar.(Ahmad)