Taron dimokaradiyya da Amurka ta kira zai kara fallasa boyayyun manufofin ta
2021-12-02 16:55:30 CRI
Tun a kwanakin baya, lokacin da mahukuntan Amurka suka bayyana aniyar su ta kiran taron da suka ce wai na “Dimokaradiyya” ne, masharhanta ke ta bayyana mabanbantan ra’ayoyi game da hakan.
Bisa kalamai da jami’an Amurka suka sha furtawa, manufar taron za ta kasance yin bita, game da nasarorin da Amurka da kawayenta suka cimma a fannin karewa, da aiwatar da salon mulkin dimokaradiyya. To amma abun tambaya a nan shi ne, shin Amurka za ta iya kasancewa duniya wani madubin dimokaradiyya, da har za ta rika kiran tarukan kare dimokaradiyyar?
Amsar wannan tambaya a bayyane take. Idan mun yi la’akari da yanayin da duniya take ciki a yanzu na fuskantar kalubaloli masu tarin yawa, kamar daga na koma bayan tattalin arziki, zuwa na yaduwar cutar numfashin ta COVID-19, da yadda wannan annoba ta karade kasashen duniya manya da kana, ciki har da Amurka ita kanta, inda ta yi mummunar barna. A fili take cewa Amurka ta gaza wajen shawo kan wannan matsala, da ma sauran kalubalolin dake addabar kasar a cikin gida.
A baya bayan nan, an ga yadda Amurka ke dandana kudar tsadar rayuwa, baya ga koke da sassan ’yan kasar suke yi game da rasa damar fadin albarkacin baki, da gazawa wajen tsara zabuka masu inganci, da yaduwar cin hanci, da uwa uba matsalar kare hakkin bil adama, ta yadda kawo yanzu sanadiyyar bazuwar cutar COVID-19 kadai, Amurkawa sama da dubu 800 suka rasa rayukan su.
Idan har mahukuntan Amurka su gaza wajen sauke nauyi irin na kare rayukan al’umma, suka kuma kasa daidaita matsalolin tattalin arziki da na zamantakewar al’ummar su yadda ya kamata, shin anya kuwa ya dace a wannan gaba su kira taro domin kare dimokaradiyya?
Wannan ne ma ya sa masu fashin baki da dama ke ganin cewa, bai dace sassan kasa da kasa su bari Amurka ta yi amfani da su, da sunan kare dimokaradiyya, a haifar da rarrabuwar kawuna ba. A maimakon haka, kamata ya yi a dora muhimmanci ga hadin gwiwar dukkanin sassan, wajen warware kalubalolin bai daya dake addabar daukacin bil adama, kuma lokaci zai kara fayyace boyayyun manufofin Amurka game da wannan taro da aka ce wai na “kare dimokaradiyya” ne.