logo

HAUSA

Za a bude layin dogo a tsakanin kasar Sin da kasar Laos

2021-12-02 15:48:56 CRI

Za a bude layin dogo a tsakanin kasar Sin da kasar Laos_fororder_hoto

A ranar 3 ga wata, za a kammala aikin gina layin dogo a tsakanin kasar Sin da kasar Laos, aikin da aka kwashe shekaru 5 ana gudanar da shi. Layin da aka gina bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”, ya tashi ne daga birnin Kunming na kasar Sin har zuwa birnin Vientiane, fadar mulkin kasar Laos, kuma gaba daya, tsawonsa ya kai kilomita 1035.

A gobe Jumma’a kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Laos Thongloun Sisoulith za su gana ta kafar bidiyo, domin ganin bikin kaddamar da layin dogon na Sin zuwa Laos a hukumance.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce ganawar shugabannin biyu, za ta ba da jagoranci ga aikin karfafa dunkulewar kasar Sin da kasar Laos, kuma za ta kara ingiza raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin dogon lokaci. (Maryam)