logo

HAUSA

Wani tsagin AU ya yi maraba da alkawarin da Sin ta yi a taron FOCAC a Senegal

2021-12-02 10:04:58 CRI

Wani tsagin AU ya yi maraba da alkawarin da Sin ta yi a taron FOCAC a Senegal_fororder_sin-afirka

Hukumar bunkasa ci gaban Afrika reshen kungiyar tarayyar Afrika wato AUDA-NEPAD, dake da ofishinta a Johannesburg, ta yi maraba da alkawarin da kasar Sin ta yi na taimakawa Afrika da alluran rigakafi da zuba jari da kuma aiwatar da daftarin muhimman kudurori hudu.

Shugaban AUDA-NEPAD, Ibrahim Mayaki, ya yi wannan tsokaci ne a ranar Laraba a yayin wani taro ta kafar intanet domin tattauna sakamakon da aka samu a taron ministocin dandalin FOCAC karo na takwas wanda aka gudanar a ranakun 29 zuwa 30 ga watan Nuwamba a kasar Senegal.

A cewarsa, alkawarin da kasar Sin ta yi na samar da karin alluran rigakafi abin da a yi maraba da shi ne bisa lura da irin goyon bayan da take nunawa ga Afrika a yaki da sabon nau’in cutar COVID-19 mai suna Omicron.

Ya zuwa ranar 12 ga watan Nuwamban 2021, kasar Sin ta samar da alluran rigakafin COVID-19 sama da biliyan 1.7 ga kasashe sama da 110 da kungiyoyi, wanda ya hada har da kasashen Afrika 50 da kungiyar tarayyar Afrika AU. Kasar Sin ta sanar a wajen taron ministocin FOCAC cewa, za ta samar da karin alluran rigakafin COVID-19 guda biliyan 1 ga Afrika domin cimma burin AU na yiwa kashi 60 bisa 100 na al’ummar nahiyar rigakafin nan da shekarar 2022.

Mayaki ya ce, baya tantanma huldar dake tsakanin Sin da Afrika muhimmiya ce. Abin da nahiyar ke bukata bayan da dandalin FOCAC ya cika shekaru 20 da kafuwa, yana da muhimmanci kuma akwai matukar bukatar zuba jari mai yawan gaske wanda zai kawo manyan sauye sauyen ci gaba a dukkan fannonin tattalin arzikin Afrika, ta yadda zai mayar da Afrika ta zama wata muhimmiyar shiyya a harkokin kasa da kasa kamar yadda kasar Sin ta zama.(Ahmad)