logo

HAUSA

Tsohon masanin da ya gabatar wa al’ummun duniya fasahohin yin kwaskwarima na Sin

2021-12-02 15:48:07 CRI

Tsohon masanin da ya gabatar wa al’ummun duniya fasahohin yin kwaskwarima na Sin_fororder_21

A ranar 1 ga wata, aka kaddamar da babban taron “Fahimtar Kasar Sin” na kasa da kasa a birnin Guangzhou na kasar Sin, inda aka wallafa jerin litattafai mai taken “Fahimtar kasar Sin” a hukumance.

Wannan ne karo na biyu da aka wallafa jerin litattafai masu taken “Fahimtar kasar Sin”, wanda ke kumshi da litattafai guda 11. Ciki akwai littafi mai suna “Yadda aka yi kokarin karfafa dunkulewar dukkanin bil Adama” da Gao Shangquan ya rubuta, wanda aka fi sani da “tsohon masanin yin kwaskwarima” a kasar Sin.

Gao Shangquan ya taba zama mataimakin shugaban kwamitin yin kwaskwarimar tsarin tattalin arzikin kasar Sin, wanda ya ba da nagartattun shawarwari da babbar gudummawa ga aikin yin kwaskwarima a kasar Sin. (Maryam)